*BIYAYYA GA MIJI TANA GABA DA BIYAYAYA GA IYAYE !*
TAMBAYA❓
Assalamu alaikum
Mallam ina cikin wani tashin hankali, iyayena ne suka samo min aiki, mijina ya ce ba zan yi ba, nayi nayi ya ki ya yarda, su kuma sun ce sai nayi, mahaifina ya ce idan mijin nawa ya ki yarda na yi tahowa ta na amshi posting letter na, in mijin ya gaji ya biyoni
Dan Allah mallam meye abin da ya kamata nayi?na rasa yadda zanyi
Magana ta gaskiya mijina bai rageni da komai ba, babu abin da baya min kawai dai aiki yace ba yanzu ba
Yanzu ni dai bana son na saba ma iyayena kuma bana so na ki bin umurnin mijina ya xanyi dan Allah ?
AMSA👇
Wa alaikum assalam
Ki yi kokari wajan gamsar da iyayanki, da hakurkurtar da su, Idan ba su yarda ba, ki yi biyayya ga mijinki saboda ya fi mahaifinki girman hakki a kanki.
Allah ya yi Umarni da biyayya ga iyaye a ayoyi masu tarin yawa a cikin Al'qur'ani da hadisai, saidai a wajan Mace miji yana gaba da Uba, Annabi (SAW) yana cewa: "Inda zan umarci wani ya yi sujjada ga wani, to da na umarci mace ta yi sujjada ga mijinta".
Tun da mijinki yana biya miki dukkan bukatunki, barin aikin ya zama wajibi, saboda aikin Gwamnati ga mace yana halatta ne in akwai bukata kuma ya aminta daga cakuduwa da maza .
Tafiya wajan aiki ba tare da iznin mijinki ba sabon Allah ne da keta alfarmar Shari'a, Allah ya umarci Mace da ta zauna a gidanta a aya ta (33) a suratul Ahzaab.
Allah ne mafi sani
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*
0 Comments