Kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya Kaddara, Ya Hukunta, Ya kuma Rubutawa Addinin Sa na Musulunci Bunkasa, Daukaka da Wanzuwa; haka Sahabbai ma suka ci wannan arziki, suka kuma samu wannan Alfarma ta Daukaka da wanzuwar Ambato ta hanyar rubuta su, da Ambatar su cikin buwayayyan Littafin wannan Addini da Allah Ya rubuta masa Daukaka da wanzuwa.
Don haka Dan-uwa ka daina tsammanin daina magana akan Wadannan Taurari da Allah Madaukakin Sarki Ya sanya su wani bangare na Hasken da Ya kau da Duhun jahiliyya da kafirci. Al'amarin Sahabbai daga Allah ne Dan-uwa, Shi Ya shirya musu hakan, Ya kuma tsara su zamto Surukan Annabin Sa Muhammadu Sallallahu alaihi wa Sallama, baya ga kasantuwar su Mataimaka, Abokan fadi-tashi da gwagwarmayar isar da Sakon da Allah Ta'ala Ya aiko Shi dashi na Musulunci. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:
"لَّقَدْ رَضِيَ اللَّهُ عَنِ الْمُؤْمِنِينَ إِذْ يُبَايِعُونَكَ تَحْتَ الشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمْ فَأَنزَلَ السَّكِينَةَ عَلَيْهِمْ وَأَثَابَهُمْ فَتْحًا قَرِيبًا". سورة الفتح: ١٨
Acikin Tauba ma Yace:
"وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُم بِإِحْسَانٍ رَّضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ۚ ذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ" سورة التوبة: ١٠٠
Adai cikin Tauba din Ya sake cewa:
"لَّقَد تَّابَ اللَّهُ عَلَى النَّبِيِّ وَالْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنصَارِ الَّذِينَ اتَّبَعُوهُ فِي سَاعَةِ الْعُسْرَةِ مِن بَعْدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيقٍ مِّنْهُمْ ثُمَّ تَابَ عَلَيْهِمْ ۚ إِنَّهُ بِهِمْ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ". ١١٧
Sannan acan kasa, cikin Suratul fathi Ya kara yin warawara game da suwaye Sahabban Ma'aikin Muhammadu Sallallahu alaihi wa Alihi wa Sallama; Allah Ya kara musu Yarda, Yace:
"مُّحَمَّدٌ رَّسُولُ اللَّهِ ۚ وَالَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ ۖ تَرَاهُمْ رُكَّعًا سُجَّدًا يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّنَ اللَّهِ وَرِضْوَانًا ۖ سِيمَاهُمْ فِي وُجُوهِهِم مِّنْ أَثَرِ السُّجُودِ ۚ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمْ فِي التَّوْرَاةِ ۚ وَمَثَلُهُمْ فِي الْإِنجِيلِ كَزَرْعٍ أَخْرَجَ شَطْأَهُ فَآزَرَهُ فَاسْتَغْلَظَ فَاسْتَوَىٰ عَلَىٰ سُوقِهِ يُعْجِبُ الزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ الْكُفَّارَ ۗ وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ مِنْهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا" سورة الفتح: ٢٩.
Wannan yasa Mumini bashi da zabi sai yarda da Hukuncin Allah Madaukakin Sarki, da yarda da Kaddarawar Sa. Ya kuma iya bakin sa; tare da jinkai da tausayawa Magabatan sa, musamman Abokai kuma Surukan Annabin sa Muhammadu Sallallahu alaihi wa Alihi wa Sallama, yana me aiki da horon da Alkur'ani Yayi masa nayi musu Addu'ar neman Gafarar Mahaliccin su Subhanahu wa Ta'ala; inda Yake cewa:
"وَالَّذِينَ جَاءُوا مِن بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِّلَّذِينَ آمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ" سورة الحشر: ١٠
0 Comments