Hakika burin kowanne jarumi ko jaruma mawaki ko mawakiya shine tara dubun dubatar masoya daga ko a fadin duniya, domin masoya sune babban alfaharin kowa. Nura M Inuwa da mawaki ne a cikin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wanda kuma ya kwana 2 ana damawa da shi a acikin masana'antar.
A jiya ne masoyan na Nura M Inuwa suka saka shi a cikin wani farin ciki da nishadi na musamman domin sun nuna masa a fili yanda suka damu dashi da kuma irin wakokin da yake musu.
Tun tsawon lokaci masoyan na Nura suke ta kiranshi da cewa suna bukatar sabon kundin wakoki daga gurin sa. Sai dai wasu dalilai sun hana nura ci kawa masoyan nasa wannan buri nasu, inda yaje yata basu hakuri.
To hakan ne ya sa masoyan na Nura suka fito zanga-zanga domin su nuna rashin jin dadin su saboda sun gaji da gafara sa amma basu ga ko kaho ba. Inda masoyan sukayi zuga suka je har office din mawakin, kuma sukayi rubuta kala-kala a kan takardu wadanda suke nuna suna bukatar Nuran ya fitar musu da sabon Kundi na wakokin sa.
Masoyan dai sun taru ne a bakin office din mawakin inda suke ta amsa amon cewa "Nuran dai-Nuran dai" kuma suna rera wasu daga cikin wakokin sa. Inda Nuran Ya leko ta saman bene cikin farin ciki yake ta 'dagawa masoyan nashi hannu.
Mawakin dai ya rubuta wata magana mai daukar hankali da shiga zuciya a kan wannan al'amari inda ya wallata a kan shafin sa na Instagram,
Hakika Nura M Inuwa yaji matukar dadin ganin masoyan na sa, inda yai wani rubutu a yayin wallafa lamarin, a shafinsa Na Instagram.
0 Comments