NAZARI AKAN RAYUWAR AURE! DA YADDA ZA'A GUDANAR DA ITA CIKIN SAUQI...

 

Subhanallah


NAZARI AKAN RAYUWAR AURE! DA YADDA ZA'A GUDANAR DA ITA CIKIN SAUQI...

GIRKI/ABINCIA

Abinciya zama dole a rayuwa, kulawa dashi yana gyara zamantakewa, rashin kulwa dashi kuma yana 6ata zamantakewa, dadin dadawa kuma Allah ta'ala daya haliccmu ya umarcemu da muci daga abubuwa masu dadi, Manzon Allah SAW ya tarbiyyantar damu a wurare da dama akan cin abinci, misalin hakan shine fadin Allah ta'ala _Yaku wadanda sukai imani kuci daga abubuwa masu dadi na abinda muka azurtaku dashi (Baqara 172)_ Saboda haka ina fatan wannan taqaitaccen jawabi da zan gabatar zai zamarwa Uwargida ‘ci a hankali’ ko ‘ci ki qoshi kuma baki na marmari’ ko ‘hana mai gida fita.

1) Iya Girki!,,, Anan ana nufin iya sarrafa duk abinda ya sawwaqa zuwa abu mai dadi da sanin da wanne za’a qare, da sanin irin tsawon lokacin da kowanne irin abinci ya kamata ya dauka... Misali dahuwar wake da shinkafa, ko dafa shinkafa da doya da dai sauransu.

2) Iya can-canza nau’ikan abinci!,,, Hakan yana taimakawa wajen gujewa ginsa ko qosawa idan anan can-canza abinci daga wannan kalar zuwa wancan... Sannan zanso mutane su gane cewa ba wai sai an dafa abincin gidan sarki ba, duk abinda Allah ya hore dashi za ayi amfani.

3)Kula da yin abinci mai kyau, kuma mai tsafta!!,,, Abin misali anan shine mai gida Allah ya hore masa ya kawo shinkafa baqa kuma yace yana son ayi masa tuwon shinkafa, kinga idan tuwo ne sai ki jiqa ta tunda wuri, hakan zai taimaka wurin sanyawa shinkafar tayi haske wanda zaifi bada sha’awar aci... Kwanukan cin abincin suma su zamo a tsaftace, hakan zai taimaka wajen jawo hankalin mai cin abincin, wannan kuwa zai kasance anyi da wurwuri ba sai lokacin da za’a ci abincin za’a wanke ba.

4) Rashin 6ata gida!!,,, Ya kamata uwargida ta kula sosai yayin da take girki kada ta bata gidan ko rumfar girkin ko kuma kayan da take aiki dasu a lokacin girkin. Duk sanda take aiki akan wani abu wanda yake buqatar a zubar da shara daga gareshi to sai tara sharar waje daya, sannan kuma ta debe ta da zarar ta gama da wannan abin ba wai sai ta gama girkin gaba daya ba kafin ta fara gyaran gida. Hakan nan ya kamata uwargida ta kula da jikinta wajen yin girkin, ba dole ne sai jiki ya baci ba don ana girki, matan arewa sun kasance suna zama cikin datti wai saboda su suna girki kuma wannan ba dai dai bane. Dole uwargida ta tabbatar tayi amfani da duk wani abu da zai rage mata sauqin aiki a lokacin da take yin girki _(kamar su wuqa mai kaifi, tsumman goge-goge, qyallen sauke tukunya, abin kwashe shara dss) 

5) Kulawa da lafiyar jiki lokacin girki!!,,, Ana son uwargida tayi taka-tsantsan a lokacin yin girki wajen kula da lafiyar jikinta daga wuqa, wuta, abu mai nauyi da duk wani abu dai zai iya kawo barazana ga lafiyarta.

6) Kulawa da yara da sauran mutanen gida yayin girki!!,,, Yakamata uwargida ta kula da zirga-zirgar yara da sauran mutanen gida yayin da take aikin girki, kada ta dinga ajiye abubuwa a ko ina inda yara zasu iya wasa dashi ko kuma a inda manya zasu iyayin tuntube dashi ko su taka.

7) Gama girki akan lokaci!! Yakamata uwargida ta kula da lokaci wajen kammala abinci, domin yunwa bala’ice, gama girki da wuri yana daya daga cikin abubuwan da suke jan hankalin mai gida yaso abincin kuma ya qara masa qarfi ar kawo cefane mai dadi, musamman tunda akwai kwanuka masu riqe zafi yanzu (flasks)

8) Gujewa 6arnatar da abinci da kuma dafa isashshen abin shima abin kulawa ne

ZAMU CIGABA AKAN WANNAN GA6AR, AKWAI SAURAN BAYANI*

Ku sauraremu a rubutu na gaba insha Allah

Post a Comment

0 Comments